logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya jagoranci taron kolin Sin da EU karo na 24 tare da shugabannin EU

2023-12-08 10:40:54 CMG HAUSA

 

Firaministan kasar Sin Li Qiang, da shugaban majalisar Turai Charles Michel, da shugaban hukumar Tarayyar Turai Ursula Von der Leyen, sun jagoranci taron kolin Sin da kungiyar EU karo na 24 tare, a ranar Alhamis a nan birnin Beijing.

Li ya ce, ya kamata bangarorin biyu su tsaya tsayin daka wajen yin tattaunawa maimakon yin adawa da juna, da yin hadin gwiwa maimakon raba kai, da zaman lafiya maimakon rikici, wajen tafiyar da dangantakar dake tsakanin Sin da EU.

Ya kara da cewa kasar Sin a shirye take ta yi aiki da kungiyar EU wajen tabbatar da daidaiton hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da neman fahimtar juna tare da kawar da bambance-bambance, da karafa hadin gwiwar moriyar juna da daidaito tsakanin bangarori daban-daban, da kara inganta dangantakar dake tsakanin Sin da EU, da samun moriyar juna, da kuma ba da karin gudummawa ga wadata, kwanciyar hankali, da ci gaban nahiyar Eurasian da ma duniya gaba daya.

Sun kuma yi nuni da cewa, EU a shirye take ta zama amintacciyar abokiyar huldar kasar Sin, Michel da Von der Leyen sun ce, kungiyar EU na bin tsarin ’yancin kanta, kuma a shirye take ta ci gaba da tattaunawa tare da kasar Sin, don kara fahimtar juna, da rage rashin fahimtar juna, da zurfafa hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya, noma da abinci, sauyin yanayi da kirkirarriyar basira (AI), da kuma magance kalubalen duniya tare da inganta zaman lafiya, kwanciyar hankali, da wadata a duniya. (Yahaya Yaya)