logo

HAUSA

Ma’aikatar kasuwancin Sin: Za a gabatar da dabarun gudanar da ayyukan yankin cinikayya maras shinge

2023-12-08 15:28:05 CMG Hausa

Yau Jumma’a, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira taron manema labarai, inda ya yi bayani kan “Shirin inganta bude kofar yankin ciniki maras shinge na gwaji na kasar dake Shanghai (FTZ) ta hanyar hade shi da mizanin ka'idojin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa”. Wani babban jami’in ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, ma’aikatar za ta yi hadin gwiwa da hukumomin da abin ya shafa da birnin Shanghai wajen nazari da warware matsalolin dake gabansu a yayin da suke aiwatar da shirin, ta yadda za a samu wasu kyawawan dabarun da za a iya koya daga cikinsu a nan gaba.

A nasa bangare kuma, babban jami’in kwamitin kasuwancin birnin Shanghai ya ce, kyautatuwar yanayin cinikayya a tsakanin kasa da kasa ta taimaka wa birnin Shanghai wajen cigaban harkokin cinikayya, daga watan Janairu zuwa watan Oktoba na bana, jimillar hajojin shigi da fici na birnin ta zarce Yuan triliyan 3 da biliyan 500, adadin da ya karu da kaso 1.9 bisa dari bisa na makamancin lokacin na bara. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)