logo

HAUSA

Mahukuntan Sin sun kira taron karawa juna sani don neman shawarwarin raya tattalin arziki

2023-12-08 21:51:34 CMG

Kwamitin kolin JKS ya kira taron karawa juna sani tare da sassan da ba na JKS ba, don neman ra’ayoyi, da shawarwari game da yanayin tattalin arzikin kasa a bana, da kuma ayyukan da za a gudanar badi domin raya fannin.

Yayin zaman wanda shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping ya jagoranta, ya gabatar da muhimmin jawabi, wanda a cikin sa ya ce a shekarar 2024, za a cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, kuma za ta kasance muhimmiyar shekara ta aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 14, don haka ya dace ayyukan raya tattalin arziki su kasance bisa babban tsarin neman samun ci gaba tare da wanzar da daidaito.

Shugaba Xi ya kara da cewa, ya kamata a ci gaba da bunkasa samar da ci gaba mai inganci, da zurfafa gyare-gyare da bude kofa, da ingiza matakan dogaro da kai, da karfafa fannonin kimiyya da fasaha.

Cikin wadanda suka gabatar da jawabai yayin taron akwai shugabannin kwamitocin koli na jam’iyyu 8 wadanda ba na JKS ba, da shugaban kungiyar masu masana’antu da cinikayya ta Sin ko ACFIC a takaice, da wakilin sassa marasa bin jam’iyyu. Dukkanin sassan sun amince da matsayar kwamitin kolin JKS, na nazarin halin da tattalin arzikin Sin ke ciki, da kuma shirin da ya tsara game da aiwatar ayyukan raya tattalin arzikin kasa a badi.

Har ila yau, sun gabatar da shawarwari kan batutuwan da suka shafi raya tattalin arzikin kasar, shawarwarin da shugaba Xi ya ce za a nazarce su tare da amfani da su.  (Saminu Alhassan)