logo

HAUSA

An fitar da rahoto game da nazarin yadda ake raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” ta fuskar kare hakkin dan Adam

2023-12-07 20:44:59 CMG Hausa

Asusun raya hakkin dan Adam na kasar Sin, da cibiyar nazari karkashin kamfanin dillancin labaru na Xinhua wato NCR, a yau Alhamis, sun fitar da wani rahoton hadin gwiwa mai taken "Don ingantacciyar duniya-waiwaye kan shekaru goma da suka gabata a fannin raya shawarar ‘Ziri daya da hanya daya’, a mahangar kare hakkin dan Adam."

Rahoton ya yi nuni da cewa, a shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da manufar raya shawarar "Ziri daya da hanya daya", wanda ke da nufin bunkasa ci gaba ta hanyar hadin gwiwa, da sa kaimi ga kare hakkin bil Adama ta hanyar raya kasa, da inganta neman ci gaba, da samun wadata tare, da kuma karfafa jin dadin zaman dukkan bil'adama, tsakanin kasashen dake bin shawarar, ta hanyar karfafa mu'amala da juna a matakai daban daban a dukkan fannoni.

A cikin shekaru 10 da suka gabata, a matsayin wani muhimmin dandali na gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga bil'adama, aikin raya shawarar "Ziri daya da hanya daya", ya riga ya samu halartar kasashe fiye da 150, da kungiyoyin kasa da kasa sama da 30, kana kuma ya jawo jarin da ya kai kusan dalar Amurka tiriliyan daya, tare da samar da ayyukan hadin gwiwa masu tarin yawa. Kaza lika, hakan ya samar da guraben ayyukan yi da dama ga kasashen da abin ya shafa, da kuma taimakawa dubban jama'a fita daga kangin talauci.

Rahoton ya jaddada cewa, ingantawa, da kuma kare hakkin bil'adama, lamari ne na gama-gari ga dukkan bil'adama. Kuma manufar samun bunkasuwa tare da ke kunshe cikin shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kuma nasarorin da aka cimma a fannin, ba wai sun ingiza gudummawar kasar Sin ne a fannin sa kaimi ga bunkasuwar harkokin kare hakkin bil'adama na duniya ne kadai ba, har ma da ba da gudummawar hikimar kyautata yanayin duniya, na kula da hakkin dan Adam. (Mai fassara: Bilkisu Xin)