logo

HAUSA

Sin za ta yi duk mai yiwuwa wajen shawo kan kalubalen sauyin yanayi a duniya

2023-12-07 20:43:30 CMG

A baya bayan nan, sama da kasashen duniya 100 ne suka amince da manufar ninka adadin wutar lantarki da ake samarwa da nau’o’in makamashi da ake iya sabuntawa nan zuwa shekarar 2030. Kasashen sun amince da hakan ne, yayin taron sauyin yanayi na COP28 dake gudana a hadaddiyar daular Larabawa.

Wasu daga kafofin watsa labarai da suka yi tsokaci kan hakan, sun ce kasar Sin ce daya tilo, cikin manyan kasashen duniya, ke da ainihin ikon cimma wannan buri.

Yayin taron manema labarai na Alhamis din nan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce Sin za ta ci gaba da nacewa manufofinta na ingiza samar da ci gaba mai dorewa ba tare da gurbata muhalli ba, kana za ta yi iyakacin kokarin ba da gudummawa, wajen tunkarar kalubalen sauyin yanayin duniya.

Daga nan sai Wang ya yi kira ga kasashe mahalarta taron COP28, da su cika alkawuran da aka amincewa, su ba da gudummawar cimma manufofi masu nasaba, gwargwadon halin da kasashen su ke ciki, kana su hada karfi da karfe wajen warware kalubaloli, da matsalolin da ake fuskanta, dangane da raya fannin makamashin da ake iya sabuntawa.  (SAMINU ALHASSAN)