logo

HAUSA

Jakadan shugaban kasar Sin zai halarci bikin rantsar da shugaban kasar Argentina

2023-12-07 19:33:34 CMG

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce jakadan musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping wato Wu Weihua, zai halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Argentina Javier Milei, wanda za a gudanar a ranar Lahadin karshen makon nan.

Mista Wu, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalissar wakilan jama’ar kasar Sin, zai tashi zuwa birnin Buenos Aires ne domin halartar bikin rantsuwar, bisa gayyatar gwamnatin Argentina.  (Saminu Alhassan)