logo

HAUSA

Yawan daliban da za su gama karatu daga jami’a a shekarar 2024 a kasar Sin zai kai miliyan 11 da dubu 790

2023-12-06 11:16:49 CMG Hausa

Rahotanni daga wajen taron samar da ayyukan yi da kafa kamfanoni na daliban da za su kammala karatu daga jami’a a shekarar 2024 na kasar Sin da ma’aikatar kula da harkokin albarkatun kwadago da bada tabbaci ga zamantakewar al’umma ta kasar Sin ta gudanar a jiya, na cewa, yawan daliban da za su kammala jami’a a shekarar 2024 a kasar Sin, zai kai miliyan 11 da dubu 790, wanda ya karu da dalibai dubu 210 bisa na makamancin lokacin shekarar 2023.

Ma’aikatar ilmi ta kasar Sin ta bayyana cewa, za a bullo da wasu manufofi don fadada hanyoyin samar da aikin yi, da hidima don taimakawa daliban samun aikin yi. (Zainab Zhang)