logo

HAUSA

Wang Yi: Sin da Angola sun kafa misali na hadin gwiwar kasashe masu tasowa

2023-12-06 20:38:33 CMG

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce kasashen Sin da Angola, sun kafa wani kyakkyawan misali na raya hadin gwiwar kasashe masu tasowa. Wang ya bayyana hakan ne a Larabar nan, yayin da yake zantawa da takwaransa na Angola Téte António a birnin Beijing.

Ya ce bangaren Sin a shirye yake, ya karfafa hadin gwiwa da Angola, da ingiza tsarin gina dandalin hadin kan Sin da Afirka, da gina al’ummar kut da kut ta Sin da Afirka mai makomar bai daya, da hada hannu wajen kare halastattun iko, da moriyar kasashe maso tasowa, ta yadda za a kai ga bunkasa tsarin gudanar da harkokin duniya bisa adalci, kuma kan turba mafi dacewa.

A nasa bangare kuwa, mista António cewa ya yi hadin gwiwar Angola da Sin, na amfanar dukkanin sassan, kuma yana haifar da sakamako mai kyau gare su, kaza lika manyan ayyuka na gudana yadda ake fata, wanda hakan ya ingiza kawancen dake tsakanin kasashen 2.

Mista António na gudanar da ziyarar aiki ta yini 4 a kasar Sin tun daga jiya Talata.  (Saminu Alhassan)