logo

HAUSA

Ministan wajen Sin ya yi hira da takwaransa na kasar Birtaniya ta wayar tarho

2023-12-06 11:34:23 CMG Hausa

A jiya Talata, mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, mista Wang Yi ya zanta da takwaransa na kasar Birtaniya David Cameron ta wayar tarho bisa gayyatar da ya yi masa.

Yayin zantawar tasu, Wang Yi ya ce, bisa la’akari da matsayin Sin da Birtaniya na zaunanun mambobin kwamitin sulhu na MDD, akwai babban nauyin dake wuyansu na kare zaman lafiya da tabbatar da kwanciyar hankali a duniya. Kana ci gaban huldar dake tsakanin kasashen 2, ba zai tsaya kan alfanun da al’ummun kasashen 2 kawai za su samu ba, har ma kunshi ma’anar musamman ta fuskar tabbatar da lumana da walwala a fadin duniya. Kasashen 2 za su iya zame wa junansu wata dama ta samun ci gaban kasa, don haka ya kamata bangaren Birtaniya ya dauki daidaitaccen ra’ayi kan kasar Sin, da bayar da gudunmawa ga kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2.

A nasa bangare, mista David Cameron ya ce, yanzu haka babu wata kasa ita kadai da za ta iya tinkarar kalubaloli bisa karfin kanta, saboda haka, gudanar da cudanya da hadin kai tsakanin Birtaniya da Sin, zai biya bukatun junansu. Birtaniya na son karfafa hulda tare da kasar Sin, da kara yin cudanya tsakaninsu. Kana ta yabawa kasar Sin, kan yadda take kokarin goyon bayan ra’ayin kasancewar bangarori masu fada-a-ji daban daban a duniya. Kasar Birtaniya na fatan ganin kasar Sin za ta kara taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa, da na shiyyoyi, in ji jami’in kasar Birtaniya. (Bello Wang)