logo

HAUSA

Wang Yi ya tattauna ta wayar tarho da sakataren wajen Amurka

2023-12-06 16:09:10 CMG Hausa

A yau ne, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken bisa bukatarsa.

Wang Yi ya bayyana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaran aikinsa na Amurka Joseph Biden a birnin San Francisco na kasar Amurka, inda suka tsaida burin kyautata huldar dake tsakanin kasashen biyu, wannan yana da babbar ma’ana. Muhimman ayyukan da bangarorin biyu suke fuskanta a halin yanzu, su ne aiwatar da ra’ayi daya da aka cimma a yayin ganawarsu a birnin San Francisco, da karfafa dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, ta yadda za a samu damar raya dangantakarsu mai dorewa yadda ya kamata. Wang Yi ya sake jaddada matsayin Sin kan batun yankin Taiwan, da bukatar kasar Amurka da ta magance tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, da daina nuna goyon baya ga ’yan aware na yankin Taiwan.

Hakazalika bangarorin biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan rikicin Palesdinu da Isra’ila, tare da yarda da ci gaba da musayar ra’ayi kan halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya. (Zainab)