logo

HAUSA

Ana iya fahimtar tattalin arzikin kasar Sin daga mahanga mai fadi

2023-12-06 21:41:17 CMG Hausa

Adadin motoci masu amfani da sabbin makamashi da ake kerawa da sayarwa a kasar Sin, yana kan gaba a duk fadin duniya, a cikin jerin shekaru 8, al’amarin da ya shaida habakar tattalin arzikin kasar. Wato ana iya fahimtar tattalin arzikin kasar Sin daga mahanga mai fadi.

Saurin karuwar tattalin arziki shi ne wani muhimmin ma’auni. Daga watan Janairu zuwa Satumbar bana, tattalin arzikin kasar Sin ya karu da kaso 5.2%, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, yayin da irin wannan karuwa a kasar Amurka, da yankin kasashe masu amfani da kudin EURO ya kai kaso 2.4% da kimanin 0.5%.

Tattalin arzikin kasar Sin ya karu da kaso 5%, yayin da wasu ke cewa wai tattalin arzikin kasar zai fadi warwas. Ita kuwa Amurka, tattalin arzikinta ya karu ne da kaso 2%, yayin da wasu ke cewa wai kasar tana samun bunkasuwa sosai.

Game da kalaman wasu mutane na shafawa tattalin arzikin kasar Sin bakin fenti, shugaban gidauniyar George H.W. Bush ta raya dangantakar Amurka da Sin, Neil Bush bai amince da hakan ba, inda a cewarsa, akwai abubuwa da yawa da ka iya taimakawa habakar tattalin arzikin kasar Sin, kana, gwamnatin na da cikakkun hikimomi na daidaita manufofi, don haka yana da yakini sosai ga makomar tattalin arzikin kasar Sin.

Ya kamata wasu mutane daga kasashen yammacin duniya su saurari maganar Neil Bush, saboda shafawa saura bakin fenti, ba zai taimaka maka ba, amma ci gaban kasar Sin mai dorewa zai amfani ga dukkanin fadin duniya. (Murtala Zhang)