logo

HAUSA

Sin ta harba tauraron dan adam na gwajin fasahar intanet na tauraron dan adam

2023-12-06 11:24:31 CMG Hausa

Kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan adam, don gwada fasahohin intanet na tauraron dan adam zuwa sararin samaniya, daga wani yankin teku da ke kusa da birnin Yangjiang na lardin Guangdong dake yankin kudancin kasar Larabar nan.

An yi amfani da roka mai suna Smart Dragon-3(SD-3) wajen harba tauraron da misalin karfe 3 da mintuna 24 na safe agogon Beijing, kuma ya shiga falaki kamar yadda aka tsara.

Wannan shi ne karo na biyu da aka yi amfani da rokar Smart Dragon,bayan na farko da aka harba a watan Disamban da ya gabata, inda aka harba taurarin dan adam 14 zuwa sararin samaniya.(Ibrahim)