logo

HAUSA

Taron MDD ya zartas da kudurin adawa da girke makamai tun farko a sararin samaniya

2023-12-06 20:28:18 CMG Hausa

An zartas da wani daftarin kudurin da Sin da Rasha suka gabatar, na adawa da girke makamai tun farko a sararin samaniya, bisa kuri’u masu rinjaye da aka kada a babban taro karo na 78 na Majalisar Dinkin Duniya.

Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Laraba cewa, hakan ya shaida matsayin kasa da kasa, na goyon-bayan gudanar da shawarwari kan takardar dokokin kasa da kasa, game da hana yaduwar makamai a sararin samaniya, da adawa da girke makamai a sararin samaniyar.

Jami’in ya ce, abun bakin-ciki shi ne, akwai wasu kasashe da ba sa so a taka musu birki, a fannin raya karfin soji a sararin samaniya, kuma sun dade da dakile hanyar da za’a bi wajen yin shawarwari kan takardar dokokin bisa hujjar raya fasahohi, har ma sun nuna shakku kan matsaya daya da aka cimma, dangane da haramta yin takarar makamai a sararin samaniya.

Sai dai a nata bangare, kasar Sin tana fatan wadannan kasashe za su bayyana aniyarsu ta fannin siyasa, da gyara kuskure, tare da nuna goyon-baya, da halartar shawarwari dangane da takardar dokokin takaita yaduwar makamai a sararin samaniya, da kiyaye tsarin duniya bisa tushen dokokin kasa da kasa. (Murtala Zhang)