logo

HAUSA

Kasar Sin: Yawan kunshin kayayyaki da aka isar a kasar ya kafa wani sabon tarihi

2023-12-05 11:29:18 CMG Hausa

Hukumar kula da harkokin isar da sako ta kasar Sin ta fitar da bayanai a yau 5 ga wata, inda ta bayyana cewa, ya zuwa ranar 4 ga watan Disamba, yawan kunshin kayayyaki da aka isar a kasar Sin ya zarce guda biliyan 120 a bana, wanda ya kafa wani sabon tarihi mai girma.

Tun daga shekarar 2021, yawan kunshin kayayyaki da ake isarwa a kasar Sin na shekara-shekara ya zarce guda biliyan 100 a cikin shekaru uku a jere, kuma a karon farko ya zarce kunshi guda biliyan 120, wanda ya nuna irin wadatar da kasuwancin isar da kayayyaki na kasar Sin ke da shi, da kuma nuna kyakkyawar ci gaba a kasuwan kayan masarufi na kasar Sin. (Muhammed Yahaya)