logo

HAUSA

Sin ta sake zama memba a rukunin A a kungiyar IMO

2023-12-05 21:28:12 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ya bayyana a yau Talata 5 ga watan nan cewa, kasarsa ta sake zama memba a rukunin A, a kungiyar kula da harkokin teku ta kasa da kasa wato IMO a takaice, al’amarin da ya zama babbar amincewa da kasa da kasa ke nunawa kasar Sin, ganin yadda take bayar da gudummawa ga daidaita harkokin teku na duniya, da samar da dauwamammen ci gaba ga harkokin jigilar kayayyaki a yankunan teku.

A ranar 1 ga watan da muke ciki ne aka gudanar da zaben kasashe membobi a sabon zagaye, a yayin babban taron kungiyar IMO karo na 33 a birnin London na kasar Birtaniya, inda Sin ta sake zama memba a rukunin A, bisa kuri’u masu rinjaye da aka jefa mata, kuma karo na 18 da Sin din ke zama memba tun daga shekara ta 1989. (Murtala Zhang)