logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci bikin bude taron karawa juna sani na tunawa da cika shekaru 75 da wallafa sanarwa kan hakkin dan Adam na duniya

2023-12-05 19:18:31 CMG Hausa

A yau Talata 5 ga wata ne, memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya halarci bikin kaddamar da taron karawa juna sani na kasa da kasa a birnin Beijing, don tunawa da cika shekaru 75, da wallafa “sanarwa kan hakkin dan Adam na duniya”, tare da gabatar da jawabi.

Jami’in ya ce, sanarwar na da babbar ma’ana a tarihin ci gaban wayewar kan bil’adama, wadda ta taka muhimmiyar rawa ga bunkasar harkokin kiyaye hakkokin dan Adam a duniya.

Wang ya ce jam’iyyar kwaminis, gami da gwamnatin kasar Sin, sun dade suna mayar da hankali sosai kan ayyukan rayawa, gami da kiyaye hakkokin dan Adam, bisa la’akari da hakikanin halin da kasar take ciki. Kaza lika turbar da kasar Sin ta zaba don raya hakkin dan Adam, ta dace da halin da take ciki, gami da muradun al’ummarta, kuma Sin za ta ci gaba da kokari a wannan fanni ba tare da kasala ba.

Jami’in ya kuma jaddada cewa, kasarsa za ta nuna hazaka wajen halartar ayyukan daidaita harkokin duniya, da aiwatar da sanarwa kan hakkin dan Adam na duniya, da ci gaba da tallata akidun daukacin bil’adama, ciki har da zaman lafiya, da bunkasuwa, da daidaito, da adalci, da demokuradiyya, da ‘yanci, ta yadda sana’ar kare hakkin dan Adam ta duniya za ta kara bunkasa. (Murtala Zhang)