logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da wakilan diflomasiyya daga EU, da kasashe mambobin kungiyar

2023-12-05 10:25:07 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang yi ya gana da wakilan diflomasiyya a kasar Sin daga kungiyar Tarayyar Turai (EU) da kasashe mambobinta.

Wang, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da kungiyar EU ta nuna kyakkyawar alamar farfadowa da ci gaba a karkashin jagorancin manyan tsare-tsare na shugabannin bangarorin biyu.

Wang ya kara da cewa, ya kamata kasar Sin da EU su kokarta tare don tabbatar da nasarar taron, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da EU zuwa wani sabon matsayi da sabbin fata.

Yayin da yake jadadda jawabin Wang, shugaban tawagar EU a kasar Sin, da wakilan diflomasiyya na kasashe mambobin kungiyar EU a kasar Sin, ya bayyana cewa, kungiyar EU ta kuduri aniyar raya dangantaka mai ma’ana da inganci dake tsakanin kasashen EU da kasar Sin, kuma a shirye take ta kiyaye mutuncin juna, da ci gaba da tuntuba da yin shawarwari da kasar Sin.

Kungiyar ta EU ba ta da niyyar raba gari da kasar Sin, kuma tana fatan kulla huldar moriyar juna tare da kasar Sin a fannin tattalin arziki da cinikayya, a cewar su. (Muhammed Yahaya)