logo

HAUSA

Sin Ta Yi Amfani Da Rokar CERES-1 Y9 Wajen Harba Sabbin Taurarin Dan Adam

2023-12-05 09:28:13 CMG Hausa

A yau ne, kasar Sin ta yi amfani da rokar CERES-1 Y9 na kasuwnci, wajen harba sabbin taurarin dan Adam guda biyu daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar, zuwa sararin samaniya kamar yadda aka tsara.

An harba taurarin ne da misalin karfe 7 da mintuna 33 na safe agogon birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Kuma wannan shi ne karo na 11 da aka yi amfani da rukunin rokar CERES-1, wajen harba tauraron dan Adam zuwa sararin samaniya. (Ibrahim)