logo

HAUSA

Wang Yi ya gabatar da ta’aziyyar rasuwar Kissinger

2023-12-05 20:49:47 CMG

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ziyarci ofishin jakadancin kasar Amurka dake Sin a Talatar nan, inda ya gabatar da ta’aziyyar rasuwar tsohon sakataren wajen Amurka Henry Kissinger.

Yayin da yake bayyana alhinin rasuwar tsohon jami’in, Wang ya ce Dr. Kissinger tsohon abokin kasar Sin ne, kuma Sinawa za su ci gaba da tunawa da gudummawar da ya baiwa kasar su, a fannin daidaita alakar Sin da Amurka. Ya ce lokaci ya tabbatar, kuma zai ci gaba da tabbatar da ingancin matakan siyasa da Dr. Kissinger da jagororin Sin suka aiwatar, wadanda suka dace da moriyar al’ummun kasashen biyu, da dacewar hakan da lokuta, da burin sassan kasa da kasa.

Daga nan sai Wang ya jaddada cewa, shugabannin Sin da Amurka sun cimma nasarar ganawa a San Francisco, inda suka yi tattaunawa mai zurfi kan muhimman batutuwa masu fa’ida, da ginshikan al’amura masu nasaba da bunkasa alakar sassan biyu, kana sun cimma daidaito kan jerin abubuwa masu muhimmanci, wadanda za su taimaka wajen ingantawa, da bunkasa huldarsu yadda ya kamata. Har ila yau, jami’in ya yi kira ga sassan biyu, da su aiwatar da daidaiton da shugabannin kasashen biyu suka cimma.   (Saminu Alhassan)