logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Belarus

2023-12-04 14:39:05 CMG Hausa

A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Belarus Alexander Lukashenko, a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Yayin ganawarsu, shugaba Xi na kasar Sin ya ce, kasar Sin tana goyon bayan kasar Belarus, kan niyyarta ta bin turbar raya kasa da ta dace da yanayin da kasar ke ciki, da kin yarda da yadda wasu bangarori daga waje ke neman tsoma baki cikin harkokin gidan kasar. Sin na son ci gaba da kokarin hadin kai tare da Belarus, don mara wa juna baya kan harkoki daban daban, da zurfafa huldar dake tsakaninsu a kai a kai, da karfafa hadin gwiwa karkashin tsarin MDD, da na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO, da kokarin aiwatar da shawarwari masu alaka da ci gaban tattalin arzikin duniya, da tabbatar da tsaro, da kare al’adu da wayewar kai a duniya, gami da sa kaimi ga aiki na gina bil Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya a duniya.

A nasa bangare, shugaba Lukashenko na kasar Belarus ya ce, kasarsa za ta tsaya kan kokarin kyautata huldar dake tsakaninta da kasar ta Sin, da karfafa hadin gwiwa mai amfanawa junansu, don kara daukaka matsayin abokantakar da ta kasance tsakanin kasashen 2, wadda ta shafi daukacin manyan tsare-tsare na fannoni daban daban. (Bello Wang)