logo

HAUSA

Sin da Singapore za su gudanar da tarukan karfafa hadin gwiwa

2023-12-04 21:42:35 CMG

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce kasar Sin da Singapore, za su gudanar da jerin taruka game da hadin gwiwar dake tsakaninsu, yayin ziyarar da mataimakin firaministan Singapore Lawrence Wong zai gudanar a kasar Sin, tsakanin ranaikun Talata zuwa Juma’a.

Wang Wenbin ya kara da cewa, mataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang, tare da mista Wong, wanda kuma shi ne ministan kudin Singapore, za su jagoranci taro na 19, na majalissar hadin gwiwar Sin da Singapore a birnin Tianjin a ranar Alhamis.  (Saminu Alhassan)