logo

HAUSA

Za a gudanar da taron jagororin Sin da EU a Beijing

2023-12-04 18:58:58 CMG

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce kamar yadda aka amince tun a baya, za a gudanar da taron shugabannin Sin da kungiyar tarayyar Turai ta EU karo na 24, a ranar Alhamis ga watan nan na Disamba a birnin Beijing.

Cikin wata sanarwa game da hakan, Hua ta ce yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai gana da shugaban majalissar Turai Charles Michel, da shugabar hukumar zartaswar tarayyar Turai Ursula von der Leyen.

Kaza lika, sanarwar ta ce firaministan kasar Sin Li Qiang, da Michel, da von der Leyen, za su yi hadin gwiwar jagorantar taron dake tafe.  (Saminu Alhassan)