logo

HAUSA

Shugaba Xi ya yi kira da a ingiza muhimmiyar rawa da kundin mulkin kasa ke takawa a fannin jagorancin kasa

2023-12-04 21:11:10 CMG

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a kara azama wajen ingiza muhimmiyar rawa da kundin tsarin mulki ke takawa a fannin jagorancin kasa.

Cikin wani umarnin shugaba da ya gabatar a Litinin din nan, albarkacin ranar kundin tsarin mulkin kasa karo na 10 da ake bikin ta a yau din, shugaba Xi ya jaddada muhimmancin martaba iko, da kimanta darajar kundin tsarin mulkin kasa, yayin da ake yayata manufofin ingantawa da bunkasa shi.

Ya ce kundin tsarin mulkin kasa shi ne tushen ayyukan shari’a, wanda jam’iyya ke amfani da shi wajen jagorancin kasa, kana shi ne tsarin shari’a na koli ga siyasa da zaman rayuwar al’ummar kasa.

Daga nan sai shugaban na Sin ya jaddada muhimmancin kara azama wajen kyautata tsarin shari’a na gurguzu mai halayyar musamman na Sin, wanda ke da kundin tsarin mulkin kasa a matsayin jigonsa, tare da ci gaba da kyautata yadda ake aiwatarwa da sanya ido kan sa.   (Saminu Alhassan)