logo

HAUSA

Sin ta taimaki Masar wajen harba wani tauraron dan Adam zuwa sararin samaniya

2023-12-04 21:00:35 CMG Hausa

Da misalin karfe 12 da minti 10 na yau Litinin 4 ga watan nan ne cibiyar harba taurarin dan Adam ta Jiuquan ta kasar Sin, ta yi nasarar amfani da rokar Long March-2C, don harba wani tauraron dan Adam mai lamba MISRSAT-2 zuwa sararin samaniya, inda tauraron ya shiga falaki yadda ya kamata.

Za’a yi amfani da tauraron dan Adam din ne don taimakawa kasar Masar gudanar da bincike kan albarkatun kasa, da biyan bukatunta a fannoni daban-daban, ciki har da aikin gona, da aikin gandun daji, da gine-ginen birane da garuruwa, da kiyaye muhalli, da sa ido kan bala’u da sauransu. (Murtala Zhang)