logo

HAUSA

Sin ta taya Andry Rajoelina murnar sake zama shugaban kasar Madagascar

2023-12-04 19:54:24 CMG Hausa

Bisa sakamakon karshe da babbar kotun tsarin mulkin kasar Madagascar ta fitar kwanan nan, Andry Rajoelina ya sake lashe babban zaben kasar, da kashi 58.96 bisa dari na kuri’un da aka jefa.

Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Litinin 4 ga watan nan cewa, kasarsa ta taya Rajoelina murnar sake zama shugaban Madagascar.

Wang ya ce, Sin ta dade tana maida hankali sosai ga raya huldar abokantaka tare da Madagascar, inda ta yi fatan kara kokari tare da sabuwar gwamnatin Madagascar, don zurfafawa, gami da fadada mu’amala da hadin-gwiwarsu a karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kuma tsarin FOCAC, wato dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka, da kara samar da ci gaba ga dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni.

Har wa yau, jami’in ya sanar da cewa, bisa goron gayyatar da memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gabatar musu, ministocin harkokin wajen Angola da Mali, wato Téte António, da Abdoulaye Diop, za su kawo ziyarar aiki kasar Sin, tun daga ranar 5 zuwa 8 ga watan Disamban nan, da ranar 6 zuwa 10 ga watan nan. (Murtala Zhang)