logo

HAUSA

Gwamnatin Argentina ta baiwa shugaban CMG babbar lambar yabo

2023-12-03 14:41:52 CMG Hausa

Kwanan nan ne ofishin jakadancin kasar Argentina dake kasar Sin, ya shirya bikin musanyar nasarorin hadin-gwiwar kasashen Sin da Argentina a fannin al’adu, inda gwamnatin Argentina ta karrama mataimakin shugaban sashin fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar wato CMG a takaice Mista Shen Haixiong, da wata babbar lambar yabo ta samun manyan nasarori a fannin musanya, da hadin-gwiwar al’adu tsakanin kasa da kasa. A madadin shugaban Argentina Alberto Fernández, jakadan kasar dake kasar Sin, Gustavo Sabino Vaca Narvaja, ya mika lambar yabon ga Mista Shen.

A jawabin sa ta kafar bidiyo, shugaban kasar Argentina, Mista Alberto Fernández ya bayyana cewa, a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, har kullum al’ummar kasar Sin na tare da al’ummar Argentina, inda suke kokarin karfafa zumunta tsakaninsu. Kuma a batun kare cikakken yankin kasa, Argentina na nunawa kasar Sin goyon-baya, da taimakawa munufar cudanyar bangarori daban-daban a duniya, don tinkarar kalubale kafada da kafada.

A nasa jawabin kuwa, Mista Shen Haixiong ya ce CMG ya kafa tsarin hadin-gwiwa na dogon lokaci, tare da manyan kafafen yada labarai da dama na Argentina. Kana kuma zai kara kokarin bayar da gudummawa ga inganta musanyar al’adu tsakanin Sin da Argentina, da bunkasa dangantakarsu a sabon zamanin da muke ciki. (Murtala Zhang)