logo

HAUSA

Shahararren masanin kasar Sin: Rasuwar Kissinger ta karfafa gwiwar bude sabon babi ga alakar kasa da kasa

2023-12-03 20:10:05 CMG Hausa

Mataimakin shugaban kungiyar nazarin manyan tsare-tsaren gudanar da kirkire-kirkire, da samar da ci gaba ta kasar Sin, kana mataimakin shugaban cibiyar nazarin shawarar “ziri daya da hanya daya”, da daidaita harkokin duniya a jami’ar Fudan ta kasar, Mista Huang Renwei, ya zanta da wakilin CMG, wato babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, inda ya ce, tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka, marigayi Henry Kissinger ya wakilci wani zamani, amma rasuwarsa ba ta tafi da zamanin ba, akasin haka, ya karfafa gwiwar bude sabon babi ga alakar kasa da kasa.

An gudanar da wani taron kasa da kasa mai taken “fahimtar kasar Sin” na shekara ta 2023, daga ranar 2 zuwa 3 ga watan Disamban nan a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin, inda Huang ya fadi cewa, mutane da yawa sun ambaci sunan Kissinger, da tunawa da shi bayan rasuwarsa a ranar 29 ga watan Nuwamban bana a yayin jawabansu a wajen taron.

A ganin Huang, kamar yadda marigayin ya ce, duk da cewa akwai matsaloli da dama, amma in dai an bude kofa, tare da gudanar da shawarwari za’a iya samo mafita.

Marigayi Henry Kissinger, aminin arziki ne na al’ummar kasar Sin, wanda ya sha kawo ziyara kasar fiye da sau dari, kuma ziyararsa ta karshe a kasar ta faru ne a watan Yulin bana. (Murtala Zhang)