logo

HAUSA

Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin gaggauta gina Shanghai zuwa birnin zamani na gurguzu

2023-12-03 21:10:36 CMG

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin gaggauta gina birnin Shanghai zuwa birnin kasa da kasa na zamani mai salon gurguzu, ta hanyar mayar da hankali ga gina cibiyoyin kasa da kasa na raya tattalin arziki, da hada hadar kudade, da cinikayya, da kirkire-kirkiren kimiyya.

Shugaban na Sin ya yi tsokacin ne yayin rangadin da ya gudanar a birnin na Shanghai, tsakanin ranaikun Talata zuwa Asabar. (Saminu Alhassan)