logo

HAUSA

Xi Jinping ya taya murnar kaddamar da dandalin Liangzhu

2023-12-03 16:25:56 CMG Hausa

Yau Lahadi 3 ga wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon murnar kaddamar da dandalin tattaunawa da ake kira “Liangzhu Forum” karo na farko.

Sakon shugaba Xi ya nuna cewa, wurin tarihi na Liangzhu dake lardin Zhejiang na kasar Sin, ya shaida tarihin wayewar kan kasar na tsawon shekaru dubu 5, kuma abu ne mai matukar daraja a cikin wayewar kan dukkanin duniya. A cikin tarihin dan Adam na dogon lokaci, wayewar kan al’ummar kasar Sin ta rika kirkiro sabbin abubuwa, tare da dagewa kan al’adun gargajiya, al’amarin da ya sa ta samu nasarori da dama. Wayewar kan kasar Sin a bude take, kana tana samun karuwa babu tsayawa, da shigo da mabambantan wayewar kan kasashe daban-daban.

Xi ya kuma jaddada cewa, girmama juna, da nuna wa juna goyon-baya, hanya ce madaidaiciya da ake bi wajen raya wayewar kan bil’adama. Ya kuma yi fatan bangarori daban-daban za su yi amfani da dandalin Liangzhu, da zurfafa shawarwarin al’adu tsakanin kasashen dake halartar shawarar “ziri daya da hanya daya”, da aiwatar da shawarar inganta wayewar kan duniya, da fadada musanya a wannan fanni, da yayata akidun wayewar kai bisa adalci, da yin koyi da shawarwari tare, da yin hakuri da juna, ta yadda mabambantan wayewar kai za su wanzu cikin jituwa, da taimakawa juna, da karfafa samun fahimtar juna, da sada zumunta tsakanin al’ummomin kasashe daban-daban. (Murtala Zhang)