logo

HAUSA

Xi ya aike da wasikar taya murna ga taron fahimtar kasar Sin

2023-12-02 16:23:41 CMG Hausa

A yau Asabar ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron fahimtar kasar Sin da ya gudana a birnin Guangzhou, da ke lardin Guangdong na kudancin kasar Sin.

A yayin da farfadowar duniya ke fuskantar rauni da kuma tashe-tashen hankula daga sassan duniya, dan Adam ya tsinci kansa a tsaka mai wuya a tarihi. Xi ya ce, abu ne mai matukar muhimmanci kasashen duniya su hada kai don tinkarar kalubaloli daban-daban na duniya, da inganta ci gaba tare, da kyautata jin dadin bil’Adama.

"Don fahimtar kasar Sin, muhimmin abu shi ne fahimtar zamanantar da kasar Sin, kasar Sin tana ciyar da kyakkyawar manufar gina kasa mai girma da kuma farfado da al'umma daga dukkan bangarori ta hanyar zamananatarwa irin ta kasar Sin, da sa kaimi ga gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga bil'Adama,” a cewar Xi. "Makomar kasar Sin tana da nasaba sosai da makomar bil'Adama baki daya."

Ya kara da cewa, kasar Sin na neman bunkasuwa mai inganci ta hanyar bude kofa ga kasashen waje, kana kasar Sin za ta ci gaba da samar da tsarin kasuwanci mai inganci, da tsarin kasuwancin duniya mai inganci bisa nagartaccen tsarin doka, kana za ta ci gaba da fadada bude kofa ga hukumomi dangane da dokoki da ka'idoji da daidaitattun tsarin gudanarwa. (Yahaya)