logo

HAUSA

Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan bangarori don gina duniya mai tsabta

2023-12-02 16:24:03 CMG Hausa

Mataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, a matsayin babbar kasa mai tasowa mai sanin ya kamata, kasar Sin a shirye take ta yi aiki da dukkan bangarori domin gina duniya mai tsafta da kyau.

Ding, wakilin shugaban kasar Sin Xi Jinping na musamman, kuma zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a wajen taron kolin kula da yanayi na duniya a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Ding ya mika fatan alherin shugaba Xi ga UAE na karbar bakuncin taron. Ya ce, shekaru takwas da suka gabata, Xi ya yi aiki tare da shugabannin wasu kasashen duniya wajen cimma yarjejeniyar Paris tare da azama da hikimar siyasa, kuma ya fara wata sabuwar tafiya ta hadin gwiwa a duniya don magance sauyin yanayi.

A ko da yaushe kasar Sin tana kiyaye alkawuran da ta dauka, kuma tana ba da muhimmiyar gudummawa ga harkokin jagorancin duniya, a cewar Ding, ya kara da cewa, kasar Sin ta sa kaimi ga hadin gwiwar kasa da kasa kan harkokin kiyaye muhalli, da juyin juya halin makamashi, da sauyin yanayi, tare da tallafawa kasashe masu tasowa wajen kara karfinsu na tinkarar sauyin yanayi. (Yahaya)