logo

HAUSA

Masani: Zamanantarwa irin ta Sinawa wani sabon salo ne na wayewa

2023-12-02 16:43:25 CMG Hausa

Wakilin gidan talabijin na kasar Sin CGTN ya yi hira da Liu Yangsheng, babban mai bincike a Taihe Think Tank, a taron fahimtar kasar Sin dake gudana a Guangzhou dake kudancin kasar. Inda Liu ya yi nuni da cewa, hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin wani sabon salo ne na wayewa, wanda ya sha bamban da hanyar zamanantarwa ta kasashen yamma ta mulkin mallaka, da kwace da kuma mamaya. Kasar Sin na samun ci gaba ta hanyar zaman lafiya da lumana. Nasarar da kasar Sin ta samu a fannin fasahar yanar gizo, da makamashi mai tsafta, da hanyoyin sufuri na fasahar zamani, na baiwa kasashe masu tasowa karin zabin fasaha da sabbin damammaki na raya kasashen duniya. Liu Yangsheng ya bayyana cewa, domin kasashen duniya su fahimci kasar Sin, ya kamata a jajirce wajen karyata munanan bayanai da karairayi game da kasar Sin. Ya ba da misali da cewa, Amurka da kasashen yammacin duniya akai-akai suna tsoma baki cikin harkokin tekun kudancin kasar Sin bisa hujjar kiyaye abin da ake kira "'yancin zirga-zirga a teku". Duk da haka, a cikin shekaru 50 da suka wuce, ba a taba yin wani katsalandan ga 'yancin zirga-zirga a yankin tekun kudancin kasar Sin ba, kuma zargin da kasashen yammacin duniya ke yi na karya ne kawai. (Yahaya)