logo

HAUSA

Xi ya yi rangadi a ofishin kwamandan rundunar tsaron teku na yankin tekun gabashin kasar Sin

2023-12-01 19:40:45 CMG Hausa

A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci ofishin kwamandan rundunar tsaron teku na yankin tekun gabashin kasar Sin dake karkashin rundunar 'yan sandan kasar.

Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya jaddada cewa, za a inganta karfin kare hakkin teku, da aiwatar da dokokin teku. (Yahaya)