logo

HAUSA

Sin za ta karfafa alaka da bunkasa hadin gwiwa da Kazakhstan

2023-11-30 14:42:31 CMG Hausa

Mataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang, ya ce kasar sa a shirye take ta yi aiki tare da Kazakhstan, wajen aiwatar da kudurorin da shugabannin kasashen biyu suka amincewa, kana za ta goyi bayan cimma manyan nasarori a fannin gina shawarar “Ziri daya da hanya daya” ko BRI, tare da ingiza huldar abokantaka, da hadin gwiwa daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare zuwa mataki na gaba tsakanin ta da Kazakhstan.

Ding Xuexiang ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin da yake zantawa da shugaban Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev a birnin Astana, a wani bangare na ziyarar aiki da ya gudanar a kasar a ranaikun Lahadi da Litinin.

Yayin zantawar tasu, mista Tokayev ya ce Kazakhstan na rike hannu biyu-biyu da hadin giwar raya shawarar “Ziri daya da hanya daya”, tana kuma maraba da kamfanonin Sin da su zuba jari a kasarsa.

Baya ga ganawa da shugaban Kazakhstan, Ding ya kuma zanta da firaministan Kazakhstan Alikhan Smailov, ya kuma yi jagorancin hadin gwiwar taro na 11, na kwamitin hadin gwiwar Sin da Kazakhstan tare da mataimaki na daya na firaministan Kazakhstan Roman Sklyar. (Saminu Alhassan)