logo

HAUSA

Ding Xuexiang ya kai ziyara Turkmenistan

2023-11-30 21:27:35 CMG Hausa

Mataimakin firayin ministan kasar Sin Ding Xuexiang ya kai ziyara kasar Turkmenistan tsakanin ranar 28 zuwa ta 29 ga wannan wata, inda ya yi ganawa da shugaban kasar Serdar Berdimuhamedov, kuma ya yi shawarwari da mataimakin firayin minista kuma ministan harkokin wajen kasar Rashid Meredov, daga baya suka jagoranci taron hukumar hadin gwiwar Sin da Turkmenistan karo na 6 tare.

Kafin wannan, Ding Xuexiang ya taba kai ziyara kasar Kazakhstan kuma ya jagoranci taron hukumar hadin gwiwar Sin da Kazakhstan karo na 11. (Jamila)