Basirar Henry Kissinger abu mai daraja ne ga Amurka
2023-11-30 21:50:20 CMG HAUSA
Jiya Laraba, tsohon abokin al’ummar Sinawa, tsohon ministan harkokin wajen kasar Amurka Henry Kissinger ya rasu yana da shekaru 100 da haifuwa. A matsayin dan siyasa mafi muhimmanci bayan yakin duniya na biyu, Henry Kissinger ya taka rawa wajen ingiza tuntubar Sin da Amurka a harkokin da suka shafi diflomasiyya da ma shiga tsakanin halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya da dai sauran fannoni.
A halin yanzu, huldar Sin da Amurka na fuskantar mawuyancin hali da kalubale, Amurka na matukar bukatar dan siyasa kamar Henry Kissinger, wanda ya yi watsi da yin takara tsakanin jami’iyyu daban-daban a Amurka, da kuma amincewa da yabawa tarihi da al’adun kasar Sin, ban da wannan kuma, ya duba ‘yan siyasa dake da alaka da muradun bai daya tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata, da ma ingzia bangarorin biyu da su magance wahalhalu da samun ci gaban huldar kasashen biyu. (Amina Xu)