logo

HAUSA

Sin ta fitar da takardar bayani game da dabarun warware rikicin Isra’ila da Falasdinawa

2023-11-30 11:32:20 CMG Hausa

A yau Alhamis ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wata takardar bayanai, mai kunshe da matsaya, da shawarwarin Sin game da dabarun warware rikicin Falasdinawa da Isra’ila.

Takardar ta ce fadan da ya barke a baya bayan nan tsakanin sassan biyu, ya haifar da mummunar asarar rayukan fararen hula, tare da ta’azzara yanayin jin kai. Kaza lika hakan ya haifar da damuwa tsakanin sassan kasa da kasa.

A lokuta mabanbanta, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha fayyace matsayar kasar sa game da rikicin, yana mai jaddada bukatar tsagaita bude wuta nan take, da kawo karshen fadan baki daya, da tabbatar da damar kai kayan agajin jin kai, kana da kare fadadar tashin hankali. Har ila yau, shugaba Xi ya nuna cewa, hanya mafi dacewa ta warware wannan rikici ita ce kafa kasashe biyu masu cin gashin kai, kana kasashen duniya su yi gamayyar tabbatar da zaman lafiya, su yi aiki tare wajen warware batun Falasdinu bisa adalci ba tare da bata lokaci ba.

Bisa kudurorin MDD, kwamitin tsaron majalissar na da alhakin wanzar da zaman lafiya da tsaro tsakanin kasa da kasa, don haka ya zama wajibi kwamitin ya sauke nauyin dake wuyan sa game da batun Falasdinawa.

Game da hakan, Sin ta gabatar da shawarwari 5. Ta daya a aiwatar da cikakken matakin dakatar da bude wuta, da kawo karshen fada baki daya. Ta biyu a tabbatar da kare rayukan fararen hula. Ta uku a tabbatar da samar da agajin jin kai ga masu bukata. Ta hudu a kyautata tsarin shiga tsakani. Kana shawara ta biyar a warware dukkanin matsaloli ta hanyar siyasa.  (Saminu Alhassan)