logo

HAUSA

Ma'aikatar tsaron Sin: Sojojin 'yantar da jama'ar kasar ba za su yi sakwa-sakwa wajen kare ikon kasa ba

2023-11-30 19:20:43 CMG Hausa

A yau ne kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin, Kanar Wu Qian, ya bayyana a gun taron manema labarai cewa, Taiwan wani yanki ne mai muhimmanci da ba za a iya raba shi da kasar Sin ba, kuma batun Taiwan na kan gaba a cikin muhimman batutuwan kasar Sin. Duk wanda ke son raba yankin Taiwan da kasar Sin ta kowace fuska, rundunar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin ba za ta taba amincewa ko ta yi masa sakwa-sakwa ba.

Bugu da kari, ya kuma bayyana cewa, kasar Sin na mai da hankali sosai kan dangantakar soji tsakanin Sin da Amurka. Kuma rundunar sojojin kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Amurka bisa la'akari da aiwatar da matsayar shugabannin kasashen biyu, da yin mu'amala da hadin gwiwa bisa ka'idojin mutunta juna, da zaman lafiya, da hadin gwiwar samun nasara tare, da sa kaimi ga zaman lafiya da daidaiton ci gaban dangantakar soji tsakanin kasashen biyu. (Yahaya)