logo

HAUSA

Sin na ba da gudummawa wajen samar da abinci da tsarin samar da kaya a duniya

2023-11-29 11:38:33 CMG Hausa

An bude bikin baje kolin inganta tsarin samar da kaya na kasa da kasa na Sin, wato bikin CISCE karo na farko jiya a birnin Beijing. A yayin baje kolin, an gudanar da dandalin tattaunawa bisa jigon “samun ci gaba maras gurbata muhalli, gina makomar aikin noma tare”, yawancin baki sun mayar da hankali kan inganta ci gaban aikin gona mai dorewa maras gurbata muhalli, da gudanar da tattaunawa a matakai daban-daban bisa fannonin da suka kware.

A yayin dandalin, masana sun bayyana cewa, hada kimiyya da fasahar bayanai da fasahohin masana’antu da kuma aikin noma mai zurfi, “aikin noma” ya zama abin mai muhimmanci wajen sake gina aikin noma na zamani da inganta ci gaba mai dorewa ba tare da gurbata muhalli ba, a halin yanzu, aikin noma na Sin yana samun ingantaccen ci gaba mai dorewa ba tare da gurbata muhalli ba.

Song Juguo, mataimakin shugaban cibiyar inganta cinikayyar noma ta ma’aikatar aikin noma da raya kauyuka ta Sin, ya bayyana cewa, gwamnatin Sin ta tsaya tsayin daka kan kare gonakin da fadinsu ya kai kadada miliyan 120, kuma an kafa gonaki masu inganci da fadinsu ya kai zarce kadada miliyan 66. An kuma sami girbin hatsi a cikin shekaru 19 a jere, kuma yawan hatsin da aka samu, ya kai fiye da tan miliyan 650 a duk shekara cikin jerin shekaru 8 da suka gabata, kuma yawan wadatar kai na abincin ya kai 100% , kana yawan wadatar kai na hatsi ya wuce 95%. Hakika an sami wadatar hatsi, kuma kasar Sin ta cimma burinta na tabbatar da samar da isassun kayayyakin abinci da kanta. 

Sin ta tsaya tsayin daka kan aiwatar da manufar raya kasa ta hanyar bayar da muhimmnci ga "Muhalli”, ba wai kawai ta samu nasarar warware matsalar ciyar da al'ummarta fiye da biliyan 1.4 da kanta ba, har ma ta taka muhimmiyar rawa wajen kare tsaron abinci da tsarin samar da kaya cikin lumana a duniya. (Safiyah Ma)