logo

HAUSA

OECD: GDPn Sin zai karu da kashi 5.2 a 2023

2023-11-29 20:08:50 CMG Hausa

An yi hasashen cewa, ainihin GDP na kasar Sin zai karu da kashi 5.2 cikin dari a shekarar 2023, a cewar rahoton hasashen tattalin arziki da kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki da raya kasa (OECD) ta fitar a ranar Laraba.

Rahoton hasashen tattalin arzikinta na baya-bayan nan ya yi hasashen karuwar GDPn duniya da kashi 2.9 cikin 100 a shekarar 2023, sannan kuma za a samu raguwa kadan zuwa kashi 2.7 a shekarar 2024 da kuma wani dan ci gaba zuwa kashi 3 cikin dari a shekarar 2025.

Rahoton ya ce ana sa ran Asiya za ta ci gaba da daukar nauyin ci gaban duniya a shekarar 2024 zuwa ta 2025, kamar yadda ta yi a shekarar 2023. (Yahaya)