logo

HAUSA

Sin tana inganta bude kofa ga waje da ci gaban tattalin arzikin duniya

2023-11-29 19:39:33 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron manema labaru a yau cewa, baje kolin hanyoyin samar da kayayyaki na kasa da kasa na kasar Sin, shi ne baje kolin kasa da kasa na farko a duniya da ya mai da hankali kan hanyoyin samar da kayayyaki. Kuma wani sabon dandali ne ga kasar Sin na sa kaimi ga bude kofa ga kasashen waje, da bunkasa tattalin arzikin duniya, wanda ya jawo kamfanoni da cibiyoyi 515 na cikin gida da na waje suke halarta.

Wang Wenbin ya kara da cewa, kasar Sin na dagewa wajen sa kaimi ga bude kofa ga waje, da sa kaimi ga gina bunkasuwar tattalin arzikin duniya, kuma a shirye take ta yi hadin gwiwa tare da dukkan bangarori, wajen tabbatar cewa hanyoyin samar da kayayyaki ga masana’antun duniya sun kasance masu juriya, inganci, da karfi, tare da ba da gagarumar gudummawa don inganta farfadowar tattalin arzikin duniya da ci gaban duniya da wadata. Kasar Sin na fatan 'yan kasuwa daga kasashe daban-daban za su taka rawar gani wajen sa kaimi ga daidaita ayyukan masana'antu da hanyoyin samar da kayayyaki a duniya, da samar da karin sauki da kariya ga kamfanoni daga kasashe daban-daban don zuba jari da bunkasuwa a kasar Sin. (Yahaya)