logo

HAUSA

Dole ne bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan sun koma matsayar da aka cimma a shekarar 1992

2023-11-29 14:05:02 CMG Hausa

Ofishin dake lura da batutuwan yankin Taiwan na majalisar gudanarwar Sin, ta gudanar da taron ’yan jarida na yau da kullum a yau Laraba, inda kakakin ofishin Chen Binhua ya bayyana cewa, batun yankin Taiwan ya dade da zama mai matukar muhimmanci cikin harkokin dangantakar Sin da Amurka. 

A yayin ganawar shugabannin Sin da Amurka a San Francisco kwanan baya, shugaban Sin Xi Jinping ya bayyana matsayar gwamnatinsa game da batun yankin na Taiwan ga bangaren Amurka, inda ya jadadda cewa, ya kamata bangaren Amurka ya gudanar da wasu hakikanin ayyuka don nuna adawa ga “ yunkurin ’yancin kan yankin Taiwan”, kamar daina samar da makamai ga yankin Taiwan, da kuma nuna goyon baya ga dinkewar kasar Sin cikin lumana. A nasa bangare kuwa, shugaban Amurka Joseph Biden, ya sake nanata alkawarin da ya yi a yayin ganawarsa da shugaba Xi Jinping a bara a tsibirin Bali na Indonesiya, inda ya ce gwamnatinsa ba za ta goyi bayan neman “’yancin kan” Taiwan.

Chen ya bayyana cewa, yunkurin neman “’yancin kan Taiwan” ya gurgunta yanayin zaman lafiya a mashigin tekun Taiwan, kuma zai yi mummunan tasiri ga yanayin kwanciyar hankali ga yankunan Asiya da Pasifik. Ya ce idan ana son dangantakar bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan ta kasar Sin su koma kan hanya da ta dace, ta samun ci gaba cikin lumana, da kuma kare zaman lafiya da kwanciyar hankali na mashigin tekun Taiwan, dole ne a koma matsayar da aka cimma a 1992, wadda ta nuna manufar kasar Sin daya tak. (Safiyah Ma)