logo

HAUSA

Ministan Wajen Sin Ya Jaddada Shawarar Kafa Kasashe 2 A Matsayin Hanyar Warware Rikicin Falasdinu Da Isra’ila

2023-11-29 14:58:52 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya jaddada shawarar kafa kasashe 2 masu cin gashin kai a matsayin hanyar warware rikicin Falasdinu da Isra’ila. Yana mai cewa har kullum, kasar Sin na goyon bayan zaman lafiya, da kare mutuntaka, da dokokin kasa da kasa yayin da ake kokarin kawo karshen rikicin sassan biyu.

Har ila yau, mista Wang ya ce kasarsa na fatan za a kira karin manyan taruka masu tasiri, wadanda za su haifar da cimma matsayar wanzar da zaman lafiya cikin gaggawa, ta yadda za a shata taswirar kafuwar kasashe 2 masu cin gashin kansu.

Domin cimma wannan nasara, Wang Yi ya gabatar da shawarwari 3, da suka hada da kawar da yiwuwar sake farwa juna da yaki, da bayar da tabbacin cikakkiyar damar shigar da kayayyakin jin kai cikin Gaza. Kana a sake dawo da shawarar nan ta kafa kasashe biyu masu cin gashin kai ba tare da bata wani lokaci ba.  (Saminu Alhassan)