logo

HAUSA

Sin ta kasance mai fafutuka wajen inganta tsarin tafiyar da yanayin duniya

2023-11-28 19:58:29 CMG Hausa

A yau ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi bayani kan halin da tashar samar da wutar lantarki bisa hasken rana mafi girma a duniya da kamfanonin kasar Sin suka gina a Hadaddiyar Daular Larabawa ke ciki a wani taron manema labarai. Ya ce, tashar samar da wutar lantarkin ta kara yawan adadin makamashi mai tsabta a UAE zuwa sama da kashi 13 cikin dari daga cikin daukacin makamashin kasar. Kasar Sin ta kasance mai fafutuka wajen tafiyar da tsarin yanayin duniya, ba kawai ta mallaki tsarin samar da wutan lantarki mai tsafta mafi girma a duniya ba, har ma tana yin kokarinta wajen ba da taimako ga sauran kasashe masu tasowa a wannan fanni. Ayyukan makamashi mai tsafta kamar tashar wutar lantarki mai aiki da karfin iska ta Sachel da ke Pakistan, da tashar samar da wutar lantarki mai aiki da hasken rana ta Garissa dake Kenya, misalai ne na yadda kasar Sin ke karfafa hadin gwiwar kasa da kasa a fannoni dakile sauyin yanayi.

Dangane da shirin kasar Sin na baya bayan nan game da tafiyar da fasahar na’urori masu sarrafa da kansu wato AI a duniya, Wang Wenbin ya ce, gaba daya bangarorin kasa da kasa sun yi imanin cewa, shirin ya dace da bukatun kasashe daban-daban wajen bunkasa fasahar, kuma ya ba da gudummawa ta musamman wajen inganta ci gaban fasahar.

Dangane da batun tilastawa tsarin hada-hadar kasuwancin kasashe da Amurka ta aiwatar, Wang Wenbin ya ce, matakin da Amurka ta dauka na yin illa ga ka'idojin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, da gurgunta tsaro da zaman lafiyar masana'antu da samar da kayayyaki a duniya, matakin ba ya da farin jini kuma ba zai yi nasara ba. (Yahaya)