logo

HAUSA

Darajar yarjeniyoyin da aka cimma yayin baje kolin cinikayyar yanar gizo da aka yi a Sin ta zarce dala biliyan 21

2023-11-28 10:47:57 CMG Hausa

Sashen kula da harkokin cinikayya na Hangzhou, babban birnin lardin Zhejiang na kasar Sin, ya sanar da cewa, manyan kamfanoni sun cimma yarjeniyoyin cinikayya 32 da darajarsu ta kai sama da yuan biliyan 155.8, kwatankwacin dala biliyan 21.89, yayin baje kolin harkokin cinikayya ta kasa da kasa ta yanar gizo karo na biyu da aka kammala a birnin.

Baje kolin mai taken “cinikayya ta yanar gizo, hanyar shiga duniya” ya gudana ne daga ranar 23 zuwa 27 ga wata. Ya kuma ja hankalin kungiyoyin kasuwanci da hukumomin kasa da kasa 68, tare da kamfanoni sama da 800. Haka kuma, kasashen Finland da Afrika ta Kudu, sun samu gayyata ta musamman a matsayin manyan baki.

Yayin taron na yini 5, an kuma tattauna kan batutuwan da suka hada da gudanar bayanai tsakanin kasa da kasa da hada-hadar kudi ta yanar gizo da kuma tsarin tsaron yanar gizo. Har ila yau, an gudanar da shirye-shirye sama da 100 tare da gabatar da sabbin hidimomin da kayayyakin fasahohin zamani a karon farko.

Karo na uku na baje kolin zai gudana daga ranar 25 zuwa 29 ga watan Satumban 2024. Kuma a nan gaba, baje kolin zai rika gudana a Hangzhou a karshen watan Satumba. (Fa’iza Mustapha)