logo

HAUSA

Ya kamata The British Museum ta mayar da kayayyakin al'adu da aka sace

2023-11-28 11:18:54 CMG Hausa

Daga ranar 26 ga wata ne, firaministan Girka Kyriakos Mitsotakis, ya kai ziyara Burtaniya. A wata hira da ya yi da BBC, ya bukaci gidan adana kayan tarihi na Burtaniya, da ya mayar da sassakan marmama na Parthenon. Kasar Girka ta dade tana kira ga gidan adana kayan tarihi na Burtaniya, da ya mayar da wannan sassakar Dutse, amma ya ki.

Gidan tarihi na Burtaniya, gidan baje kolin tarihin mulkin mallaka na Burtaniya ne. Yawancin tarin abubuwan da aka jigbe a gidan, sheda ce ta ganimar da Burtaniya ta kwasa daga kasashen ketare. Wannan ya hada da kayayyakin tarihi na kasar Sin kusan dubu 23, wadanda galibi ake yiwa lakabi da "halastattu" amma a zahiri an samo su ne daga yaki, sata ko saye ta bayan fage. 

A cikin shekarun da suka gabata, a kokarin ganin an kwato kayayyakin al'adun da aka sace, kasashe da dama ciki har da kasar Sin, ba su daina bin wadannan kayayyakin tarihi da aka sace daga gidan tarihi na Burtaniya da gwamnatin Burtaniya ba, kuma sun yi kokarin kare al’adun gargajiyar kasar da na al’umma da kawar da ragowar alamomin mulkin mallaka, wanda a zahiri wani bangare ne na yunkurin ’yan mulkin mallaka na kasa da kasa. Duk da haka, Burtaniya ta ki mayar da kayayyakin tarihi bisa dalilin "kare lafiyar kayayyakin al'adu". Zamanin mulkin mallaka ya shude har abada. Don haka ya kamata bangaren Burtaniyya ya fuskanci halascin bukatun kasashe da dama tare da gaggauta mayar da kayayyakin al'adu da aka sace. Ya kamata tarihin mulkin mallaka na Burtaniya ya kasance cikakke kuma a sanya shi cikin tarihi yadda ya kamata. (Ibrahim Yaya)