logo

HAUSA

An bude bikin baje kolin hanyoyin samar da kayayyakin kasa da kasa na kasar Sin na farko

2023-11-28 19:11:16 CMG Hausa

A yau ne aka bude bikin baje kolin hanyoyin samar da kayayyakin da ake amfani da su na kasa da kasa na kasar Sin karo na farko wato CISCE a birnin Beijing, wanda ya kasance baje kolin farko a duniya a matakin kasa da ya mai da hankali kan hanyoyin samar da kayayyaki.

A wannan baje kolin, wakilan 'yan kasuwa da suka halarci taron sun yi musayar ra'ayi mai zurfi a cikin taken "Hade kasashen duniya da samar da makoma tare", kuma sun cimma jerin matsaya, tare da kafa shirin "Shawarar Beijing kan hanyoyin samar da kayayyaki ga masana'antun duniya”

A cewar shirin, 'yan kasuwa za su ci gaba da tabbatar da karkon hanyoyin samar da kayayyaki ga masana'antun duniya. Da yin riko da ka'idodin kasuwa, da habaka cinikayya da saukake ‘yancin hannun jari, da habaka wadatar kayan aiki, da karfafa tsarin hadin gwiwar rarraba kwadago na duniya, da kiyaye hanyoyin samar da kayayyaki ga masa’antun duniya tare. (Yahaya)