logo

HAUSA

Komai kankantar mataki na zaman lafiya ya cancanci karfafawa

2023-11-27 19:39:01 CMG Hausa

A yau, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a wani taron manema labarai cewa, tun bayan da Hamas da Isra’ila suka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta, bangarorin biyu sun saki kashi na uku na mutanen da suke tsare da su. Komai kankantar matakin da zai kai ga zaman lafiya ya cancanci karfafawa, kuma ya kamata a shawo kan babbar matsalar kare fararen hula. Rikici tsakanin Falasdinawa da Isra’ila na wannan karo ya kwashe sama da kwanaki 50, wanda ya haddasa asarar dimbin rayuka da kuma munanan bala’o’in jin kai. Bangaren Sin ya sha nanata cewa tashin hankali ba zai samar da tsaro na gaskiya ba, kuma karfi ba zai iya samar da dawwamammen zaman lafiya ba. Kasar Sin na maraba da duk wani yunkuri da zai taimaka wajen inganta tsagaita bude wuta da sassauta halin da ake ciki.

Wang Wenbin ya kuma gabatar da halin da ake ciki game da taron ministocin harkokin wajen Sin da Japan da Koriya ta Kudu da ya gudana a baya-bayan nan.

Ya ce, sassan uku na Sin, da Japan, da Koriya ta Kudu, sun yi imanin cewa, kamata ya yi su nace kan aiwatar da matsayar shugabannin kasashen kamar "batun makomar hadin gwiwar Sin da Japan da Koriya ta Kudu cikin shekaru goma masu zuwa", tare da amincewa da samar da yanayi mai armashi ga taron shugabannin kasar Sin da Japan da Koriya ta Kudu da kuma hanzarta shirye-shiryen da suka dace. Ya kamata bangarorin uku su yi aiki tare, su kusanci juna, da samar da yanayi mai kyau don samun sakamako mai kyau na taron shugabannin. (Yahaya)