logo

HAUSA

Sin za ta jagoranci taron manyan jami’ai na kwamitin tsaron MDD game da batun Falasdinu da Isra’ila

2023-11-27 16:08:16 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce a matsayin ta na jagorar karba karba ta kwamitin tsaron MDD a watan nan na Nuwamba, Sin za ta kira taron manyan jami’ai na kwamitin tsaron MDD game da batun Falasdinu da Isra’ila a ranar Laraba 29 ga watan nan.

Wang ya ce mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai isa birnin New York domin jagorantar taron na kwamitin tsaro. (Saminu Alhassan)