logo

HAUSA

Ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya tattauna kan takardun da suka shafi inganta ci gaban zirin tattalin arzikin kogin Yangtze

2023-11-27 16:00:12 CMG Hausa

A yau ne, ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya gudanar da wani taro, inda ya yi nazari kan ra'ayoyi da matakan da suka dace, don kara sa kaimi ga bunkasuwar zirin tattalin arzikin kogin Yangtze da kuma dokokin JKS kan harkokin waje. Babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, shi ne ya jagoranci taron.

Taron ya yi nuni da cewa, tun bayan aiwatar da dabarun raya zirin tattalin arzikin kogin Yangtze, an samu gagarumin sauye-sauye a yanayin muhalli, da na ci gaba, hadewar yankuna da sauran bangarori na yankunan da abin ya shafa. Kuma ingancin ci gaba ya kyautatu a kai a kai, kana yanayin ci gaba yana kara kyau. (Ibrahim)